Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Taron wanda shi ne irinsa na shida, ya hada shugabanni da gwamnatoci kasashe kimanin 80 wadanda rabinsu sun fito ne daga Afrika.
Alakar dake tsakanin nahiyoyin gudu biyu na daga cikin ajandar wannan taron.
An kuma tsara kananen taruruka da shugabannin zasu jagoranta tare da kwararu domin tattauna batutuwan da suka shafi bayar da tallafi dominci gaba, da tsaro da kuma tabbatar da mulki na gari.
Sai kuma batutuwan da sukla shafi kiwon lafiya, ilimi, samar da sauyi ta hanyar amfani da makamashi, da kuma tattalin arziki.
Kwanaki gabanin taron, Shugabar hukumar gudanarwar ta Kungiyar Tarayyar Turai yayin wata ziyara a Senegal ta yi alkawarin cewa Kungiyar Tarayyar Turai za ta samar da kimanin kudin Euro miliyan 150,000 domin fadada kayyayakin jin dadin rayuwa a nahiyar Afirka.
342/